Libya: "Yan Ci-Rani 119 Sun Tsira Daga Cin Ruwa
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato kakakin sojojin ruwan Libya, Ayuba Kasim yana sanar da ceto 'yan ci-ranin 119 a yau Laraba
AYub Kasim ya kara da cewa; Tuni an dauki Mutanen 119 zuwa sansanin da ke yankin Tajurah a kusa da birnin Tripoli, babban birnin kasar.
Wata kididdiga ta hukumar kasar Libya ta ambaci cewa daga farkon watan Maris zuwa yanzu an tseratar da mutane 6000 daga nutsewa a ruwa.
Kasar Libya yanya ce mai muhimmanci ta 'yan ci-rani masu son shiga turai.
Masu fasakwaurain mutane suna amfani da rashin tsaron da ake da shi a kasar Libya domin jigilar masu son shiga kasashen turai ta hanyar da ba ta dace ba.
A shekarar 2017 da ta gabata dubban yan ci-rani daga nahiyar Afirka ne su ka halaka acikin ruwan kasar Libya.