Mufti Libiya Ya Soki Saudiyya Da UAE Saboda 'Makircin Da Suke Kullawa'
Muftin kasar Libiya yayi kakkausar suka ga abin da ya kira irin makudan kudaden da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa suke kashewa wajen biyan bukatun Sahyoniyawa da kuma haifar da rashin tsaro da fitina a yankin Gabas ta tsakiya da kuma Arewacin Afirka.
Kafafen watsa labaran kasar Libiya sun jiyo Sadiq Al-Ghariani, muftin kasar Libiya, cikin wata makala da ya rubuta inda yayin da yake kakkausar suka dangane da irin makirce-makircen da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa suke kulla wa kasar Libiyan da kuma yankin baki daya ya bayyana cewar: Saudiyya da UAE suna amfani da kazamtattun dukiyarsu wajen haifar da fitina a arewa maso kudancin Libiya, wanda matukar ba a kawo karshen hakan ba, to kuwa za a fuskanci ci gaba da rarrabuwan kai a kasar.
Muftin na Libiya ya ci gaba da cewa abubuwan da wadannan kasashe biyu suke yi wajen biyan bukatun makiya musulunci abin kunya ne yana mai cewa maimakon su yi fada da makiya Musulunci, sai suka koma suna haifar da fitina a kasar Libiya da zubar da jinin mutanen Yemen da kuma fada da duk wasu masu gwagwarmaya da yahudawan sahyoniya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da malamai da masanan kasar Libiya suke Allah wadai da irin bakar siyasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa a kasar ba.