An Fara Gudanar Zaben Shugaban Masar A Wajen Kasar
An Fara gudanar da zaben shugaban kasar Masar a kasashen ketare, kafin fara gudanar da zaben a cikin kasa.
Rahotanni daga kasar ta masar sun ce hukumar zaben kasar ta bayar da bayanin cewa, tun a jiya Juma'a aka bude wuraren kada kuri'a guda 139 a ofisoshin jakadancin kasar Masar guda 124 a kasashen duniya daban-daban.
'yan kasar ta Masar da suke zaunea wadannan kasashe suna da damar zuwa su kada kuri'unsu domin zabar dan takarar da suke bukata, kuma za a ci gaba da gudanar da zaben na Masar a wajen kasar ne har tsawon kwanaki uku.
Daga cikin fitattun 'yan takara azaben shugaban kasar na Masar, akwai shugaban kasar mai ci Abdulfattah Sisi, sai kuma shugaban jam'iyyar Algad, Musa Mustafa Musa.