Saiful Islam Gaddafi Zai Tsaya Takarar Shugabancin Kasar Libiya
(last modified Tue, 20 Mar 2018 05:50:17 GMT )
Mar 20, 2018 05:50 UTC
  • Saiful Islam Gaddafi Zai Tsaya Takarar Shugabancin Kasar Libiya

Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar nan ba da jimawa ba, dan tsohon shugaban kasar Kanar Mu'ammar Gaddafi, Saiful Islam Gaddafi, sai sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar.

Kafafen watsa labaran kasar Libiya sun jiyo Aiman Buras, babban jami'i mai kula da lamurran Saiful Islam Gaddafin yana fadin cewa nan ba da jimawa ba Saiful Islam din zai sayar da tsayawarsa takarar shugabancin kasar Libiyan a zaben shugaban kasar da za a gudanar.

Jami'in ya kara da cewa manufar Saiful Islam na tsayawa takarar ba ita ce neman mulki ko matsayi ba, face dai kokari wajen sake gyara kasar bayan da aka rusa ta tun bayan kifar da gwamnatin mahaifinsa da aka yi a shekara ta 2011.

A watan Yunin shekarar bara ta 2017 ne dai aka saki Saiful Islam Gaddafin daga inda ake tsare shi tun bayan da aka kama shi a shekara ta 2011 biyo bayan kifar da gwamnatin mahaifinsa da aka yi.