Kungiyar Al Shabab ta yi ikrarin kashe dakarun Amison 59
(last modified Mon, 02 Apr 2018 06:27:25 GMT )
Apr 02, 2018 06:27 UTC
  • Kungiyar Al Shabab ta yi ikrarin kashe dakarun Amison 59

Kungiyar ta'addancin ta Al Shabab ta sanar da kashe dakarun sojan wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika Amisom da na gwamnatin Somaliya 59 a wasu jerin hare haren da ta kaddamar kan rundunar a yankin Bas-Shabelle, dake kudancin Magadisho babban birnin kasar Somaliya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa rahoton cewa: a jiya lahadi, mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab da ke Somaliya sun kaddamar da hari kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na kungiyar tarayyar Afrika "AMISOM" a takaice da ke yankin Bas-Shabelle a kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar , inda suka kwashe sa'o'i akalla hudu suna fafatawa a tsakaninsu.

Majiyar rundunar 'yan sandan Somaliya ta kara da cewa: Mayakan kungiyar ta Al-Shabab sun tada wasu motoci biyu da suka makare da bama-bamai a lokacin gumurzun tare da janyo hasarar rayukan dakarun wanzar da zaman lafiya masu yawa kuma mafi yawansu sojojin kasar Uganda ne.

Mafi yawan hare haren dai, an kai su ne ta hanyar harba rokoki kan sansanonin sojin samar da zaman lafiyar na Amisom dake da sansani a yankin na Bas-Shabelle.

A cewar wani mejon sojan Somaliya Farah Osman, wasu yan kunar bakin wake 2 ne a cikin motoci suka fara tarwatsa kansu da bama bamai a kan ayarin motocin dakarun wanzar da zaman lafiyar na tarayyar Afrika da kuma kasar ta Somaliya.