Taron Kasashen Chadi, Libiya, Nijar Da Sudan Kan Hanyoyin Karfafa Matakan Tsaro
Kasashen Chadi, da Libiya, da Nijar, da kuma Sudan sun gudanar da wani taron yini guda a Birnin Yamai kan hanyoyin karfafa matakan tsaron iyakokin kasashen hudu.
Taron wanda ya hada ministocin harkokin cikin gida da takwarorin su na tsaro da masu kula da harkokin waje da manyan hafsoshin soja da jami'an samar da bayanan sirri ya maida hankali kan hanyoyin warware matsalolin da ke da nasaba da rikicin kasar Libiya.
Ministan tsaron kasar Nijar Kalla Muntari ya bayyana wa masu aiko da rahotanni cewa matsalar da Libiya ke fama da ita, yafi karfin kasa guda.
Shi kuwa sakataren harkokin wajen kasar Sudan Abdulkarim Abdulganiy ya ce maida hankali ga musanyar bayanai itace hanya mafi a'ala wajen cimma burin da aka sa gaba.
Safara makamai daga Libiya na daya daga cikin matsalolin dake addabar kasashe makobtanta, tun bayan kifar da tsohuwar gwamnatin mirigayi Mu'ammar Gaddafi a cikin shekara 2011.