Apr 23, 2018 17:35 UTC
  • Kwamandojin Dakarun Kare Juyi Da Na Sojin Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Kare Kasar Tare

Kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) da na sojojin kasar sun bayyana shirinsu na aiwatar da shiri na bai daya da nufin kara karfafa irin shirin da ake da shi na kare kasar Iran daga duk wata barazanar da za ta iya fuskanta bugu da kari kan kare manufofin kasar.

Kafar watsa labaran Sepah News ta dakarun kare juyin ta ba da rahoton cewa  a yau ne kwamandan dakarun IRGC din Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari tare da rakiyar wasu manyan kwamandojinsa suka kai ziyarar sa da zumunci helkwatar rundunar sojin ta Iran inda suka gana da babban kwamandan sojojin na Iran Manjo Janar Sayyid Abdulrahim Musawi da kuma tattaunawa da shi.

A yayin ganawar kwamandojin biyu sun bayyana jin dadinsu dangane da irin hadin kai da aiki tare da ake samu tsakanin sojoji da dakarun kare juyin inda suka bayyana shirin da suke da shi na ci gaba da aiki tare karkashin jagorancin babban kwamandan dakarun kasar ta Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Ziyarar dai tana zuwa ne a yayin da a jiya ma dai Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran din kuma babban kwamandan dakarun kasar ta Iran a wata ganawa da yayi da manyan kwamandojin soji ya jinjinawa irin hadin kai da aiki tare da ake samu tsakanin dakarun kasar ta Iran lamarin da ke ci gaba da kona ran makiya wadanda a koda yaushe suke fatan ganin an sami sabani da rarrabuwan kai tsakanin dakarun na Iran.

Tags