Libya: Bom ya tashi a kusa da garin Ra'a Lanuf
Jaridar Yaum Sabi'i ta ambato majiyar tsaron kasar Libya na cewa; harin da aka kai na kunar bakin wake ne, ya kuma ci rayukan mutane da dama da jikkata wasu.
An kai harin na jiya ne dai a daidai lokacin da sojojin kasar a karkashin janar Halifa Haftar su ka bude kai farmaki akan 'yan ta'adda a garin Darnah.
Kwanaki uku da suka gabata wani jami'in sojan kasar ta Libya Muhammad Manfur ya ce; Jiragen yaki sun kai hare-hare akan mabuyar 'yan ta'addar a cikin garin na Darnah.
Garin Darnah ya dade da shiga karkashin ikon kungiyar 'yan ta'adda da alka'ida da take amfani da sunan Majalisar Mujahidai ta Darnah.
Libya ta fada cikin rashin tsaro tun bayan kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Mu'ammar Kaddafi a 2011.