Tashin Bam Ya Hallaka Mutum 5 A Libiya
Majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da mutuwar mutum biyar sanadiyar tarwatswar wato mota da aka shaketa da bama-bamai kusa da garin Derna dake gabashin Tripoli babban birnin kasar
Majiyar ta sanar da cewa wani adadin na iyalan dake zaune a garin Derna na kan hanyarsu na barin garin, a yayin da wannan mota da aka shaketa da bama-bamai ta tarwatse, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar daga cikin iyali guda tare kuma da jikkata mutum guda.
Majiyar asibiti ta ce wata matashiya mai shekaru 18 ta jikkata sanadiyar tashin wannan Bam, kuma ya zuwa yanzu tana cikin mawuyacin hali.
A ranar Talatar da ta gabata kakakin Rundunar tsaron kasar Ahmad Massmari ya sanar da cewa dakarun janar Khalifa Haftar sun samu nasarar tsarkake mashigar garin na Derna daga 'yan ta'adda.
A ranar 7 ga watan Mayu ne Sojojin kasar Libiya suka fara kai farmaki garin na Derna dake hanun Majalisar Shura ta Mujahiden mai alaka da kungiyar AlQa'ida tun a shekarar 2011 da nufin tsarkake shi.