An Zargi Hadaddiyar Daular Larabawa Da Bawa 'Yan Ta'adda Makamai A Libiya
Rahotani sun ce hadaddiyar daular larabawa tana taimakawa 'yan ta'addar Libiya da makamai.
Kafar watsa labaran Tunus Al-an cikin wani rahoto da ta fitar ta nakalto hukumomin kasar Libiya na cewa hadaddiyar daular laraba na taimakawa yan ta'addar dake kanm iyakokin Libiya da Tunusiya a birnin Sabratha da makamai gami da kudade sannan suna kokarin tura su zuwa kasar Aljeriya domin dagula al'amuran tsaron kasar.
Ghassan Salamé Manzon musaman na MDD kan rikicin kasar Libiya ya sanar da cewa mun sha yin gargadi a game da katsa landan din kasashen waje kan rikicin kasar ta Libiya, da hakan kuma shi ne ya nada cimma matsaya tsakanin kungiyoyin siyasar kasar ta yadda za a dawo da zaman lafiya a kasar.
A nata bangare jaridar Jane IHS ta sanar da cewa hadaddiyar daular larabawa ta kafa wani sansani na jiragen sama a kusa da garin Marj dake gabashin Libiya, inda ta ce daga wannan sansani ne jiragen yakin kasar ke kai hare-hare a kasar ta Libiya.