Aug 29, 2018 06:36 UTC
  • MDD Ta Ce Dole Ne A Hukunta Masu  Hanu A Kisan Musulmi Na Kasar Myammar

Cikin wani Zaman kwamitin tsaron MDD da ya gudana a jiya Talata, Babban saktaren MDD ya bukaci a gudanar da bincike kan wadannda suke da hanu kan kisan musulmi a kasar Mymmar sannan kuma a gurfanar da su a gaban kotu.

Saktare janar na MDD António Guterres ya yi ishara kan ta'addancin da Sojojin kasar Mymmar suka aiwatar kan al'ummar musulmin na kasar sannan ya ce wannan lamari ya caccanci a gudanar da bincike na gaskiya a kansa.

A ranar Litinin din da ta gabata ce masu bincike na MDD suka gabatar da rahoto kan kisan kare dangin da aka yi wa al'ummar musulmi a kasar Myammar, inda suka bukaci a hukunta babban hafsan sojojin kasar da wasu janar guda biyar na kasar bisa laifin take hakin-bil-adama.

Har ila yau masu binciken sun bukaci kwamitin tsaron MDD ya dora takunkumi kan wadanda da ake zargi da hanu wajen kisan musulmi a kasar ta Myammar sannan a haramtawa kasar sayar makamai.

Daga ranar 25 ga watan Augustan shekarar 2017 din da ta gabata ce Sojojin kasar Myammar suka fara aiwatar da kisan kare dangi kan al'umma a jihar Rakhin na yammacin kasar, lamarin da ya zuwa yanzu yayin sanadiyar mutuwar sama da musulmi dubu 6 yayin da wasu dubu 8 na daban suka jikkata, sannan wasu sama da miliyan daya suka yi hijra zuwa kasar Bangladesh.

Tags