Waziriyar Kasar Jamus Ta Bukaci Warware Matsalar 'Yan Gudun Hijira
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32973-waziriyar_kasar_jamus_ta_bukaci_warware_matsalar_'yan_gudun_hijira
Waziriyar kasar Jamus da a halin yanzu haka take gudanar da ziyarar aiki a kasar Senegal ta bukaci daukan matakan warware matsalolin bakin haure da 'yan gudun hijira.
(last modified 2018-08-30T19:08:33+00:00 )
Aug 30, 2018 19:08 UTC
  • Waziriyar Kasar Jamus Ta Bukaci Warware Matsalar 'Yan Gudun Hijira

Waziriyar kasar Jamus da a halin yanzu haka take gudanar da ziyarar aiki a kasar Senegal ta bukaci daukan matakan warware matsalolin bakin haure da 'yan gudun hijira.

A taron manema labarai da ta gudanar da shugaban kasar Senegal Macky Sall a birnin Dakar na kasar ta Senegal a yau Alhamis: Waziriyar kasar Jamus Angela Merkel ta jaddada bukatar daukan matakan shawo kan matsalar fataucin bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai.

A nashi bangaren Macky Sall ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ci gaba da samun halakar bakin haure a tekun mediterreniya tare da jaddada bukatar samar da ayyukan yi da kyautata rayuwar mutane musamman matasa a nahiyar Afrika domin magance matsalar bakin haure.