Libya: An Cimmma Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Tsakanin 'Yan Bindiga
Gwamnatin hadin kan kasa a Libya ta sanar da cewa an cimma matsaya kan dakatar da bude wuta a tsaanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin kasar.
Shafin Jaridar Quds Al-arabi ya bayar da rahoton cewa, Abdulsalam Ashour ministan harkokin cikin gida na kasar Libya ya sanar da cewa, an shiga tsakanin masu dauke da makamai da suke fada da juna, kuma sun amince su dakatar da fada daga daren jiya Juma'a.
Firayi ministan kasar ta Libya Faiz Siraj ya dora wa kungiyoyin da suke dauke da makamai Misrata da Zantan nauyin kula da dakatar da bude wutar.
Haka nan kuma an dakatar da tashi da saukar jiragen sama a filin saukar jirage na birnin Tripoli na tsawon kwanaki biyu, sakamakon lalata wasu bangarorin filin jirgin da 'yan bindiga masu musayar wuta suka yi.
Shugabannin kabilun Libya ne suka shiga ba wajen ganin an dakatar da bude wuta tsakanin kungiyoyin 'yan bindigar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama tun daga ranar Lahadin da ta gabata.