Saiful Islam Ghaddafi Ya Gana Da Wasu Jami'an Kasashen Masar Da UAE
(last modified Tue, 18 Sep 2018 15:00:02 GMT )
Sep 18, 2018 15:00 UTC
  • Saiful Islam Ghaddafi Ya Gana Da Wasu Jami'an Kasashen Masar Da UAE

Wasu majiyoyi a kasar Libya sun bayar da bayanai dangane da wata ganawa tsakanin Saiful Islam Ghaddafi dan tsohon shugaban Libya marigayi Kanar Ghaddafi, da kuma wasu jami'an gwamnatocin masar da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Jaridar Al-arabi Al-jadid ta kasar Qatar ta bayar da rahoton cewa, ta nakalto daga wasu manyan jami'an kasar Libya cewa, a kokarin da ake yi na yin sulhu tsakanin bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar ta Libya, wasu daga cikin manyan jami'an kasashen Masar da UAE sun gana da Saiful Islam Ghaddafi a asirce, da nufin ganin ya taka rawa wajen warware rikicin da ke tsakanin wasu manyan kabilun kasar da suke dauke da makamai.

Rahoton ya ce daga cikin wadanda ake sa ran sun gana da Saiful Islam Ghaddafi har da Tahnun Bin Zayid, wanda shi ne daraktan ma'aikatar leken asiri kuma shugaban majalisar tsaron kasa a hadaddiyar daular larabawa.

Saiful Islam Ghaddafi na a matsayin wani mutum da ake ganin yana da kyakkyawar alaka da mafi yawan kabilun kasar Libya, wanda zai iya taka rawa wajen shiga tsakani domin warware rikicin da ke tsakaninsu.