Italiya: An Kammala Taron Sulhu Akan Kasar Libya
Taron na kwanaki biyu an yi shi ne a garin Palemo da ke kasar Italiya
Fira ministan kasar Italiya Giuseppe Conte ya jaddada cewa; Wajibi ne ga kasashen duniya da su mutunta hurumin da kasar Libya take da shi su daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.
Conte ya kuma bayyana cewa bai kamata a yanke kauna akan kyakkyawar makomar kasar ta Libya ba, sannan ya ce; Taron da aka yi na sulhu yana goyon bayan tsagaita wutar yaki a Tripoli sannan kuma da kokarin samar da hanyoyin tabbatar da tsaro a cikin kasar.
Daga cikin mahalarta taron da akwai kungiyoyi 38 daga kasashe duniyar 30 da su ka hada da shugabannin kasashe 10 da ministoci 20
Tun kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi da aka yi a 2011 Amurka da sauran kasashen turai suke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar ta Libya.
Bugu da kari kungiyoyi daban-daban masu dauke da makamai suna fada da juna da zummar shimfida iko akan cibiyoyin da suke samar da man fetur.