Mutane 6 Sun Mutu Sakamakon Harin Kungiyar Daesh (ISIS) A Kudancin Libiya
Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) ne sun kashe mutane 6 a wani hari da suka kai kudancin kasar Libiya a jiya Juma'a.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wata majiyar sojin kasar Libiyan tana cewa maharan dai sun kai hari da mamaye wani ofishin 'yan sanda ne da ke garin Tazerbo da ke arewacin garin Kufra inda suka bude wuta lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 6 kafin mutanen garin su fatattake su.
Shi dai wannan garin ya kasance wani wajen ya da zango ne ga masu yawon shakatawa da suke zuwa kasar Libiyan don bude ido kafin rikicin da ya barke a kasar a shekara ta 2011.
Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan kungiyar Daesh din suke kai irin wadannan hare-hare garuruwan da suke kudancin kasar Libiya tun bayan da aka fatattake su daga babbar helkwatarsu da ke garin Sirte a shekara ta 2016.