Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Da'esh Ta Kai Hari A Gabacin Kasar Libya
Kafafen watsa labarun kasar Libya sun sanar da cewa kungiyar 'yan ta'adda da Da'esh ta kai hari akan wani ofishin 'yan sanda da ke yankin kudu masu gabacin kasar
Majiyar tsaro daga yankin ta ce maharan sun kuma kone motocin 'yan sanda 15 na 'yan sanda.
Tun bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar Kaddafi a 2011 kasar Libya ta fada cikin rikicikin siyasa da tsaro.
Shekaru uku da su ka gabata, kasar ta sami gwamnatoci da majalisun dokoki biyu a tsakanin biranen Tripoli da Tubruk.
Majalisar dokokin Tubruk tana samun goyon bayan janar Halifa Haftar wanda yake jagorantar sojojin Libya, yayin da gwamnatin hadin kan kasa ta Fa'ie Siraj take samun goyon bayan kasshen turai da Amurka tana kuma da cibiya a Tripoli.
Kungiyoyin 'yan ta'adda kasar Al'ka'ida da Da'esh suna amfani da rashin jituwar da ake da shi domin fadada ikonsu.