Dec 07, 2018 09:01 UTC
  • Nijar Ta Amince Da Dokar Ba Ta Kariya Ga 'Yan Gudun Hijira Wadanda Suka Rasa Matsuguninsu

Jamhuriyar Nijar ta amince da dokar kasa ta ba da kariya da kuma taimakon mutanen da suka gudu suka bar matsugunansu saboda rikici, ko wani bala'i na daban irin su ambaliyar ruwa da fari.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce gwamnatin ta Nijar da kuma Majalisar Dinkin  Duniya ne suka tabbatar da hakan a jiya Alhamis sakamakon ci gaba da karuwar yawan 'yan gudun hijira da wadanda suka rasa muhallinsu a yankin Yammacin Afirka.

Yayin da yake magana kan hakan ministan agajin gaggawa na Nijar din Lawan Magaji ya ce 'yan majalisar dokokin kasar ta Nijar a zaman da suka yi ranar Litinin din da ta gabata sun amince da dokar wacce za ta taimaka sakamakon yawan karuwar 'yan gudun hijira da wadanda suka rasa muhallin na su a kasar ta Nijar saboda matsaloli daban-daban da ake fuskanta a kasar.

Dokar dai ta ginu bisa Yarjejeniyar Kamfala ta 2009 da kungiyar Tarayyar Afirkan ta gabatar wanda ya samar da wasu matakai na ba da kariya ga mutanen da suka rasa muhallinsu a kasashensu sakamakon matsalolin irin su yaki ko fari ko kuma ambaliyar ruwa.

 

Tags