'Yan Bindiga Sun Kwace Iko Da Rijiyoyin Man Fetur A Kasar Libya
Kamfanin Man fetur na kasar Libya ne ya sanar da cewa; Masu dauke da makaman sun kwace iko da wani wurin hakar mai mai muhimmanci wanda yake a kudu maso yammacin kasar
Tuni dai kamfanin man na kasar Libya ya kada dokar ta kwana a yankin na Sharara da aka dakatar da fitar da man daga cikinsa
Bugu da kari kamfanin man na kasar Libya ya kira yi mahukuntan kasar da su yunkura domin kare manufofin kasar
Rijiyoyin hako man fetur na Sharara suna a karkashin kamfanin Akakus ne na hadin gwiwa a tsakanin kasar Libya da Spain da kuma kamfanin Total na kasar Faransa sai kuma OMB na kasar Austria
A kowace rana ta Allah ana hako man fetur da ya kai ganga dubu 315 daga wannan wurin.
Tun bayan 2011 Libya ta rika fitar da man fetur ganga miliyan daya da 600,000 a koowace rana ta Allah