Jan 24, 2019 07:05 UTC
  • A Karon Farko 'Yan Tawayen Chadi  Da Aka Kama A Nijer Sun Bayyana

A karon farko wasu shugabannin 'yan tawayen kasar Chadi guda biyu sun bayyana tun bayan da gwamnatin Nijar ta mika su ga hannun mahukuntan kasar ta Chadi bayan kama su a garin Agadez na arewacin kasar ta Nijar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya nakalto  wata majiyar tsaron kasar ta Chadi  a jiya Laraba na cewa an tsinkayi biyu daga cikin wadannan 'yan tawaye wato Hassan Boulmaye tsohon shugaban kungiyar tawayen ta CCMSR da kuma Ahmat Yacoub Adam tsohon kakakin kungiyar a gidan kurkuku na tsakiyar birnin Ndjamena, a yayin da na uku mai suna Abdraman Issa wanda da ma ke fama da cutar siga ya rigaye mu gidan gaskiya a cewar majiyar tsaron kasar ta Chadi.  

A karshen shekara ta 2017 ne kasar ta Nijar ta kama 'yan tawayen na kungiyar CCMSR mai da'awar ceto kasar Chadi daga mulkin kama karya su uku tare da mika su a hannun mahukuntan kasar ta Chadi. 

Sai dai tun daga wancan lokaci gwamnatin kasar ta Chadi ta musanta karbar wadannan 'yan tawaye daga hannun kasar ta Nijar.

Tags