An Hallaka Daya Daga Cikin Komondojin Kungiyar Alqa'ida A Libiya
Kakakin rundunar tsaron kasar Libiya ya sanar da kashe daya daga cikin komondojin kungiyar ta'addancin nan na Alqa'ida a kudancin kasar
Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Ahmad Mismari kakakin Babban komandan dakarun tsaron Libiya a wannan Litinin na cewa jami'an tsaron kasar sun samu nasarar hallaka Adil Ahmad Al-abdali wanda ake yi masa lakabi da Abu Zubair, yayin wani sumame da suka kai garin Sabha dake kudancin kasar.
Mismari ya kara da cewa: Abu zubairi na daga cikin 'yan ta'adda mafi hadari, wanda ya shiga cikin kungiyar Alqa'ida a kasar Siriya, a shekarar 2004 an kawo shi kasar Libiya bayan da ya kwashe tsahon lokaci a gidan yari na Abu Salim.
A cewar kakakin Babban komandan dakarun tsaron Libiya a shekarar 2011, kungiyar Alqa'ida ta zabi Abu Zubair a matsayin wanda zai nemowa kungiyar sabin mayaka a kasashen arewacin Afirka ya kuma tura su zuwa kasar Siriya.
Har ila yau sanarwar ta ce Abu Zubair nada alaka da Abdul-Mun'im Salim Hasnawy na kungiyar Jabhatu-Nusra da aka hallaka a makun da ya gabata.
A jiya Lahadi ne Sojojin kasar Libiya suka sanar da tsarkaka garin Sabha daga hanun 'yan ta'adda.