An Kashe Kwamandan Kungiyar Al'Ka'ida A Kasar Libya
Kakakin sojan kasar Libya ne ya sanar da kashe wani kwamanda daga cikin kwamandojin kungiyar 'yan ta'adda ta al'ka'ida
Kakakin sojan na kasar Libya, Ahamd al-Mismari ya fada a jiya Litinin cewa; Sojojin kasar sun yi nasarar kashe Adil Ahmad al-Abdali wanda aka fi sani da "Abul Zubair" a wani hari da su ka kai a garin Sabha
Al-mismari ya kara da cewa; Mutumin da aka kashe, yana da hatsari matuka, kuma ya shiga kungiyar al-ka'ida ne a kasar Syria, kafin daga baya a 2004 ya isa kasar Libya.
Kakakin sojan na kasar Libya ya kuma ce; Abul-Zubari da aka kashe ya zama kusa mai jawo sabbin 'yan ta'adda a cikin kungiyar ta al-ka'ida daaga shekarar 2011 da yin jigilarsu zuwa kasashen Syria da kuma Libya
Da akwai alaka a tsakanin Abul-Zubair da wani kasurgumin dan ta'addar da aka kashe a Libya a makon da ya shude mai suna Abu Talha Liby
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai sojojin Libya su ka sanar da kwace garin Sabha daga hannun 'yan ta'adda
Kasar Libya ta fada cikin rashin tsaro ne tun daga 2011 da kasashen Amurka da turai su ka kifar da gwamnatin Mu'ammar kaddafi