Kasar Libiya Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Fada Da Ta'addanci A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6937-kasar_libiya_ta_kaddamar_da_sabon_shirin_fada_da_ta'addanci_a_kasar
Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar shugaban majalisar kasar Aqilah Saleh ya kirayi al'ummar kasar da su hada kai wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 19, 2016 06:33 UTC
  • Kasar Libiya Ta Kaddamar Da Sabon Shirin Fada Da Ta'addanci A Kasar

Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar shugaban majalisar kasar Aqilah Saleh ya kirayi al'ummar kasar da su hada kai wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar

Kamfanin dillancin labaran hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran ya bayyana cewar a kokarin gwamnatin kasar Libiyan na fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da suke ci gaba da cin karensu ba babbaka a kasar, shugaban majalisar wakilan kasar Libiyan Aqilah Saleh ya kirayi al'ummmomin yankuna daban-daban na kasar da su shirya yin fito na fito da kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kasar.

Har ila yau shugaban majalisar ya sanar da Manjo Janar Abdullah Al-Nazuri a matsayin gwamnan mulkin soji na yankunan da suka kama tun daga garin Darna dake gabashin kasar zuwa Bn Jawad da ke yammacin kasar.

Cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan dai sojojin kasar Libiyan sun fara samun nasarori a fadar da suke yi da 'yan kungiyar ta Da'esh a garin Sirte da ke arewacin kasar.