-
Jami'an Tsaron Sudan Sun Kashe Mutum Guda A Zanga-Zanga
Feb 18, 2019 15:45Jami'an tsaron kasar Sudan sun kashe mutum guda a zanga-zangar da ake gudanarwa akasar domin yin kira ga shugaba Albashir ya sauka daga kan shugabancin kasar.
-
Somalia Na Neman Sulhu A Takkadama Da Kenya
Feb 18, 2019 02:15Kasar Somalia na nemi a kai zuciya nesa a takkadamar da ta kunno kai tsakaninta da makobciyarta Kenya, kan yankin nan dake iyakarsu wanda ya kunshi ruwa.
-
AFCON U20 : Mali Ta Lashe Kofin Afrika Na Matasa
Feb 18, 2019 01:33Mali ta lashe kofin gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekaru ashirin, da aka kammala jiya Lahadi a filin wasa na Seyni Kunce, na birnin Yamai a Jamhuriya Nijar.
-
An Sako Daliban Da Aka Sace A Kamaru
Feb 18, 2019 01:06Rahotanni daga Jamhuriya Kamaru, na cewa an sako daliban makarantar nan kimanin 200 da aka sace ranar Asabar data gabata a birnin Bamenda dake arewa maso yammacin kasar.
-
Sudan Zata Fita Daga Matsalolin Da Take Fama Da Su_ Al-Bashir
Feb 17, 2019 15:45Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya bayyana cewa kasarsa zata fita daga matsalolin da take fama da su a halin yanzu.
-
An Kara Tsananta Tsaro A Kasar Algeria Kafin Zabubbukan Kasar.
Feb 17, 2019 15:43Jami'an tsaro a kasar Algeria wadanda suka hada da sojoji da 'yansanda sun kara tsananta tsaro a kasar Algeria a dai-dai lokacinda zabubbukan kasar yake karatowa.
-
Kisan Kiyashin Kajuru: Al-Rufa'i Ya Ziyarci Yankin
Feb 17, 2019 15:39Gwamnan Jihar Kaduna Ahmad Al-rufa'i ya ziyarci yankin da aka yi kisan kiyashi na karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a jiya Asanbar inda ya ganewa idanunsa irin asarar da aka yi .
-
AFCON_U20 : Za'a Fafata A Wasan Karshe Tsakanin Senegal Da Mali
Feb 17, 2019 07:20Da yammacin Yau Lahadi za a buga wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na matasa, tsakanin Senegal da Mali a filin wasa na Seyni Kounche da ke Yamai babban birinin Jamhuriyar Nijar.
-
An Hallaka Mayakan (IS) Bakwai A Masar
Feb 17, 2019 07:07Rundinar sojin kasar Masar, ta sanar da hallaka mayakan kungiyar (IS), guda bakwai, a yayin da suka kai hari kan wani shingen bincike na soji a arewacin yankin Sinai.
-
An Sace Dalibai 200 A Kamaru
Feb 17, 2019 06:58Rahotanni daga Kamaru na cewa wasu mayaka sun yi awan gaba da dalibai kimanin 200 a garin Bamenda dake yankin masu magana da turancin Ingilishi.