-
Shugaban Kasar Afrika Ta Kudu Ya Kafa Komitin Nemawa Kasar Jari Na Dalar Billiyon 100
Apr 17, 2018 14:39Shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kafa komitin masanan tattalin arziki da yan kasuwa don samarwa kasar jari na akalla dalar Amurka billyon 100 daga ciki da wajen kasar.
-
Murtaniya Ta Yi Allawadai Da Harin Sojan Da Aka Kai Wa Kasar Syria
Apr 17, 2018 08:42Jam'iyyar Social Democratic ta kasar Murtaniya ta fiyar da sanarwa da a ciki ta bayyana kin amincewarta da harin sojan da kasashen turai bisa jagorancin Amurka su ka kai wa Syria
-
Demokradiyyar Congo: An Kori Alkalai 200 Daga Aiki
Apr 17, 2018 08:40Radiyon kasa da kasa na Faransa ne ya bada labarin cewa shugaba Joseph Kabila ya ba da umarnin korar alkalan da suke a matsayin kaso 6 % na dukkanin alkalan kasar
-
'Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga-Zangar Sako Sheikh Zakzaky 115
Apr 17, 2018 00:33Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, sun sanar da cewa suna tsare da 'yan kungiyar harkar Musulunci a Nijeriya (IMN) su 115 sakamakon dirar mikiyar da suka yi musu jiya Litinin da nufin tarwatsa jerin gwanon da suke ci gaba da yi a birnin Abujan don bukatar a sako musu shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da gwamnatin take ci gaba da tsare shi.
-
China Ta Bayyana Goyon Bayanta Na Shirin MDD Wajen Warware Rikicin Libiya.
Apr 16, 2018 14:31Karamin jakadan China a kasar Libiya ya bayyana goyon bayan kasarsa na shirin MDD wajen warware rikicin kasar Libiya ta hanyar tattaunawa.
-
Habasha Ta Nuna Adawa Da Shiga Tsakanin Amurka Wajen Magance Rikicin Madatsar Ruwan Kasar
Apr 16, 2018 14:27Hukumomin kasar Ethiopia sun bayyana adawarsu da shigar Amurka wajen magance rikicin madatsar ruwan da kasar ke ginawa
-
'Yansanda Sun Yi Amfani Da Karfi Wajen Tarwatsa Mabiya Mazhabar Shi'a A Abuja
Apr 16, 2018 14:27A Najeriya, Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da karfi a yau domin tarwatsa jerin gwanon da magoya bayan Harkar Musulunci da masu rajin kare hakkin bil adama suke gudanarwa a Abuja, domin yin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky, yayin da wasu bayanan suka tabbatar da cewa mutane da dama sun jikkata, daya daga cikinsu yana cikin mawuyacin hali, sanan kuma an kama sama da mutane 70
-
Manyan Hafsoshin Sojan Afirka Na Taro A Najeriya
Apr 16, 2018 14:26Manyan hafsoshin sojin kasa daga sassa daban daban na Nahiyar Afrika sun fara wani taro kan sha'anin tsaro yau a Abuja babban birnin Najeriya karkashin jagorancin Amurka da nufin hada hannu tsakanin kasashen don yaki da ayyukan ta'addanci.
-
Dubban 'Yan Gudun Hijira Suna Kwarara Daga Kasar Habasha
Apr 16, 2018 07:56Fiye da mutane 700,000 ne su ka bar gidajensu daga yankunan da ake rikici akan iyakokin kasashen Habsha da Somaliya
-
An Sake Cafke Masu Zanga zanga A Nijar
Apr 16, 2018 01:52Rahotanni daga jamhuriya Nijar na cewa an cafke mutane da dama ciki har da wasu mambobin kungiyoyin fara hula biyu, biyo bayan haramtacciyar zanga zangar da aka gudanar a Yamai babban birnin kasar a jiya Lahadi.