-
An Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu A Saliyo
Mar 31, 2018 14:29A yau Asabar al’ummar kasar Saliyo suka kada kuri’a a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, wanda aka fafata tsakanin dan takarar Jam’iyya mai mulkin kasar APC Samura Kamara da kuma jagoran ‘yan adawa na SLPP Julius Maada Bio.
-
Nijar : An Kori Wasu Kansilolin Zinder
Mar 31, 2018 06:08Gwamnatin Nijar ta sanar da kokar wasu shugabannin kananan hukumomi uku da suka hada da na Guidimuni da Mirriah da kuma Dantchiao, duka a jihar Zinder saboda tafka manyan kura kurai.
-
Senegal : Lauyoyin Khalifa Sall Sun Daukaka Kara
Mar 31, 2018 06:07A Senegal, lauyoyin magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, sun sanar da cewa zasu daukaka kara kan hukuncin da kotun birnin ta yanke masa na shekaru biyar a gidan yari da kuma tarar miliyan biyar.
-
Saliyo : Ana Zaben Shugaban Kasa A Zagaye Na Biyu
Mar 31, 2018 06:06A kasar Saliyo kimanin mutane milyan uku da dubu dari ne da suka cancanci kada kuri'a ke kada kuri'a a zaben shugaban kasar a zagaye na biyu.
-
Najeriya: An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Maiduguri
Mar 31, 2018 02:21Rahotanni daga Najeriya na cewa a daren jiya Juma'a an kai harin kunar bakin wake a yankin Guna Garaj da ke birnin Maiduguri fadar mulkin jahar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
-
ٍShugabar Jam'iyyar Labour Algeria: Hakkin Al'ummar Yemen Ne Su Rama Cuta A Kan Macuci
Mar 31, 2018 02:11Shugabar jam'iyyar labour a kasar Algeria Louisa Hanoune ta bayyana cewa, hakkin al'ummar kasar Yemen ne su mayar da martani da duk abin da ya sawaka a gare su a kan duk wanda ya zalunce su.
-
Libya: Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Hari A gabacin Kasar
Mar 30, 2018 14:40An kai hari ne wani wurin binciken soja da ge garin Ajdabiya agabacin kasar ta Libya
-
Adadin Wadanda Aka Kashe A Harin Da Aka Kai Jahar Zamfara Ya Karu
Mar 30, 2018 14:26Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato jami'an gwamnatin jahar Zamfara suna fada a yau juma'a cewa; fararen hula 36 ne suka kwanta dama a harin da masu dauke da makamai su ka kai wa jahar
-
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya A Libiya Ya Yi Gargadi Kan Matsalar Tattalin Arzikin Kasar
Mar 30, 2018 06:50Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya ya yi gargadi kan matsalar tattalin arzikin kasar musamman ganin yadda wasu ke wuwushe arzikin kasar, rashin biyan kudaden haraji, fataucin kayayyaki da sauransu.
-
Osinbajo: Ba Za Mu Yi Shiru Kan Ta'annutin Gwamnatin Jonathan Ba
Mar 30, 2018 00:35Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar ba za su yi shiru dangane da irin ta'annutin da gwamnatin Jonathan ta aikata ga tattalin arzikin Nijeriya din ba, yana mai cewa wajibi ne a ci gaba da sanar da 'yan Nijeriyan irin satar dukiyar kasa da aka yi a wancan lokacin wanda shi ne dalilin da ya sanya mutane cikin kuncin da suke ciki a halin yanzu.