-
Buhari Ya Gana Da Shugabannin Majalisun Nijeriya Don Dinke Barakar Da Ta Kunno Kai
Mar 16, 2018 07:39A wani abin da ake gani a matsayin kokarin dinke barakar da ta kunno kai tsakanin fadar shugaban Nijeriya da majalisun kasar, shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriyar ya gana da shugabannin majalisun tarayyar kasar su biyu a daren jiya.
-
Shugaba Biya Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na Farko Tun 2015
Mar 16, 2018 07:38Shugaban kasar Kamaru Paul Biya a jiya Alhamis ya jagoranci taron majalisar zartarwar kasar a karon farkon tun shekara ta 2015 inda ya bukaci 'yan majalisar da su yi kokari wajen karfafa tattalin arzikin kasar da kuma ba wa jami'an tsaron umurnin su murkushe 'yan awaren kasar.
-
Kasashen Tafkin Chadi Sun Sha Alwashin Gamawa Da Kungiyar Boko Haram
Mar 16, 2018 07:38Kasashen tafkin Chadi tare da kasar Benin sun sanar da aniyarsu ta yin duk abin da za su iya wajen ganin bayan kungiyar kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram
-
Senegal: Mutane Da Dama Sun Rasu A Faduwar Wani Jirgin Sama Mai Saukar Angulu Na Soja
Mar 16, 2018 02:51Kamfanin Dillancin labarin Waj na kasar Aljeriya da ya ba da labarin ya kara da cewa; Mutane 20 suka rasa rayukansu da kuma jikkata sanadiyyar hatsarin
-
An Kai Hari Akan Tawagar Shugaban Majalisar Koli Ta Mulkin Kasar Libya
Mar 16, 2018 02:47Tashar talabijin din aljazera ta ambato ofishin Abdurrahamn Suwaihili yana cewa; An bude wuta akan ayarin motocinsa ne a yayin da yake ziyartar wasu garuruwa biyu da ke yammacin kasar
-
Masar: Shugaban Kasa Ya Yi Alkawalin Kaddamar Da Zabe A cikin Ruwan Sanyi
Mar 16, 2018 02:46Abdulfattah al-Sisi ya fada a jiya alhamis cewa; Za a yi zaben a ruwan sanyi kuma ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba.
-
Zimbabwe : Juyin Mulki Ne Aka Mini_ Mugabe
Mar 15, 2018 14:50Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya danganta cilasta mashi yin murabus a matsayin juyin mulki.
-
Kamaru : Sojoji Za Su Ci Gaba Da Daukar Mataki A Yammacin Kasa_Biya
Mar 15, 2018 14:07Shugaba Paul Biya na Jamhuriya Kamaru, ya ce dole ne sojojin kasar su ci gaba da matsa kaimi don tabbatar da doka da oda a yankin yammacin kasar na masu amfani da harshen turancin Ingila dake fama da rikici, har sai al'amura tattalin arziki da na jama'a sun daidaita.
-
Mufti Libiya Ya Soki Saudiyya Da UAE Saboda 'Makircin Da Suke Kullawa'
Mar 15, 2018 07:51Muftin kasar Libiya yayi kakkausar suka ga abin da ya kira irin makudan kudaden da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa suke kashewa wajen biyan bukatun Sahyoniyawa da kuma haifar da rashin tsaro da fitina a yankin Gabas ta tsakiya da kuma Arewacin Afirka.
-
Hukumar NJC A Nijeriya Ta Bukaci A Kori Alkalai Biyu Da Kuma Jan Kunnen Sauran
Mar 15, 2018 07:51Hukumar da ke sanya ido kan lamurran shari'a a Nijeriya (NJC) ta bukaci da a sallami wasu alkalai guda biyu a kasar kamar yadda kuma ta ja kunnen sauran alkalan kuma kan ayyukan da suke yi.