-
An Kai Harin Ta'addanci A Babban Birnin Kasar Somaliya
Nov 27, 2018 03:21"Yan sandan kasar ta Somaliya ne su ka sanar da mutuwar mutane da dama sanadiyyar harin ta'addancin da aka kai a babban birnin kasar Magadishu
-
Kasashen Jamus Da Faransa Za Su Shiga Tsakanin Rasha Da Ukraine
Nov 27, 2018 03:12Ministan harkokin wajen kasar Jamus Hayko Maas ne ya ba da shawarar cewa kasarsa tare da Faransa za su shiga tsakanin Rasha da Ukraine da suke rikici
-
"Yan Ci Rani Fiye Da 100 Sun Tsira Daga Halaka A Gabar Ruwan Libya
Nov 27, 2018 03:08Sojan Ruwan Kasar Libya ne su ka sanar da ceto da 'yan ci-ranin daga halaka a gabar yammacin ruwan kasar
-
Sojojin Saman Nijeriya Sun Kai Hare-Haren Sansanonin Boko Haram A Matsayin Martani Ga Harin Metele
Nov 26, 2018 13:56Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta sanar da kai wasu munanan hare-hare kan wani sansanin 'yan ta'addan Boko Haram a matsayin mayar da martani ga harin da 'yan kungiyar suka kai wani sansanin sojin Nijeriya da ke kauyen Metele na jihar Borno inda suka kashe sama da sojoji 100.
-
Ziyarar Idriss Deby A Isra'ila, Ta Bar Baya Da Kura A Chadi
Nov 26, 2018 07:31A Chadi ziyarar da shugaban kasar ne Idriss Deby Itmo, ya kkai a Israila ta bar baya da kura, inda wasu 'yan kasar ke aza ayar tambaya akan manufar ziyarar da kuma ko mahukuntan yahudawan ne suka bukace ta ko kuma na Chadi.
-
Burkina Faso : Janar Diendere, Ya Gurfana Gaban Kotu
Nov 26, 2018 06:49A Burkina faso yau ne, Janar Gilbert Diendere, ke bayyana a gaban wata kotun sojin Ouagadugu, bisa zargin yunkurin juyin mulkin 2015.
-
Somalia: Kungiyar Al-shabab Ta kai Hari Kan Wata Cibiyar Addini
Nov 26, 2018 02:06Kungiyar Al-shabab mai da'awar jihadia kasar Somalia, ta kaddamar da wani hari a safiyar yau a kan gidan wani malamin addini a garin Jalkayur.
-
Sudan: Jam'iyyun Siyasa Sun Nuna Rashin Amincewarsu Da Kulla Alaka Da Isra'ila
Nov 26, 2018 02:05Jam'iyyun siyasa da dama a kasar Sudan sun nuna rashin amincewarsu kan hankoron da gwamnatin kasar take yi an neman kulla alaka da Isra'ila.
-
Nutsewar Jirgin Ruwa Ta Yi Ajalin Mutum 29 A Uganda
Nov 25, 2018 13:17'Yan sanda a Uganda, sun tabbatar da mutuwar mutum 29 biyo bayan nutsewar wani jirgin ruwa a tafkin Victoria.
-
Masar : An Yanke Wa Mutum 9 Hukuncin Kisa, Kan Kashe Babban Alkali
Nov 25, 2018 12:51Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa ga mutum tara da aka samu da laifin kisan mai shigar da kara na gwamnatin kasar a cikin shekara 2015 a birnin Alkahira.