Shugaba Ruhani Ya Bar Iran Zuwa Venezuela Don Halartar Taron NAM
Da safiyar yau Juma'a ne shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bar birnin Tehran zuwa kasar Venezuela don halartar taron shugabannin kasashen 'yan ba ruwanmu (NAM) karo na 17 ga za a gudanar a can kana daga baya kuma ya wuce birnin New York inda zai gabatar da jawabi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.
A wani dan gajeren jawabi da yayi kafin tashin nasa, shugaba Ruhani yayi karin bayani dangane da muhimmancin kungiyar ta 'yan ba ruwanmu a matsayin taro na biyu mafi girma na shugabannin kasashen duniya yana mai fatan za a samu nasarori yayin taron.
Ana sa ran dai shugaba Ruhani zai gabatar da jawabi a wajen taron, kafin daga baya kuma ya mika shugabannin kama-kama na kungiyar zuwa ga takwararsa na kasar Venezuelan Nicolas Maduro na tsawon shekaru uku.
Har ila yau kuma ana sa ran shugaba Ruhanin zai wuce kasar Cuba don ganawa da shugaban kasar Raul Castro da tsohon shugaban kasar kuma shugaban juyin juya halin kasar Fidel Castro.
Kungiyar 'yan ba ruwanmu dai ta kumshi kasashe 120 da kuma wasu 21 'yan kallo.