Ruhani: Tafarkin Diplomasiyya Ce kawai Za Ta Magance Rikicin Kasar Siriya
(last modified Sat, 29 Oct 2016 16:51:44 GMT )
Oct 29, 2016 16:51 UTC
  • Ruhani: Tafarkin Diplomasiyya Ce kawai  Za Ta Magance Rikicin Kasar Siriya

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya sake bayyanar matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cewa tafarkin siyasa da tattaunawa ce kawai hanya guda daya tilo ta magance rikicin kasar Siriya.

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da jami'ar harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai  Federica Mogherini wacce ta kawo ziyarar aiki nan Iran inda ya ce wajibi ne kowa da kowa ya  san cewa amfani da karfin soji ba zai taba magance rikicin kasar Siriya ba, hanya guda kawai ta magance wannan rikicin shi ne amfani da tafarki na diplomasiyya da tattaunawa tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

Shugaban na Iran ya kara da cewa ayyukan ta'addancin da ke faruwa a kasashen Siriya da Iraki wata barazana ce ga duniya baki daya, don haka ya kirayi Tarayyar Turai din da ta yi amfani da irin tasiri na siyasa da take da shi wajen matsa wa kasashen yankin Gabas ta tsakiya da suke goyon bayan 'yan ta'addan da su dakatar da hakan da kuma toshe hanyoyin da 'yan ta'addan suke samun kudaden shigarsu.

Ita ma a nata bangaren, jami'ar harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai  Federica Mogherini ta jaddada muhimmancin hadin kai da aiki tare tsakanin Iran da kasashen Turan wajen magance rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya musamman ma a Siriya tana mai cewa hanyar diplomasiyya za ta magance wadannan rikice-rikicen.

A yau ne da Mr. Mogherini ta iso nan Tehran inda ta fara ganawa da takwaranta na Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin Iran da kungiyar Tarayyar Turan da kuma batun rikicin kasar Siriya.