Feb 08, 2017 06:46 UTC
  • Shugaba Rauhani: Wajibi Ne Al'ummar Iran Su yi Tsayin Daka Domin Fuskantar Abokan Gaba.

Shugaban na Kasar Iran ya ci gaba da cewa fitowar al'umma a yayin zanga-zangar 22 ga watan Bahman wajibi ne domin murkushe makircin makiya.

Shugaban na Kasar Iran ya ci gaba da cewa fitowar al'umma a yayin zanga-zangar 22 ga watan Bahman wajibi ne domin murkushe  makircin  makiya.

Shugaban na kasar Iran da ya ke jawabi a daren jiya talata a taron majalisar koli ta al'adun juyi, ya ci gaba da cewa:  Abun alfahari ne ace bayan shekaru 38 da cin nasarar juyin musulunci, al'ummar su ci gaba da tafiya akan tafarkin juyin cike da shauki daidai da ranakun farko na juyi.

Dr.Hassan Rauhani ya kuma yi ishara da ci gaban da aka samu a karkashin juyi a fagagen ilimi da al'adu da kuma ayyukan jin dadin al'umma da  aka ci gaba da yi.

 Shekaru 38 kenan da cin nasarar juyin musulunci a Iran a karkashin jagorancin Imam Khumain (r.a) a 1979.

Tags