Iran: Amurka Za ta Cutu Idan Ta yi Watsi Da Yarjejeniyar Nukiliya.
(last modified Tue, 28 Feb 2017 08:06:03 GMT )
Feb 28, 2017 08:06 UTC
  • Iran: Amurka Za ta Cutu Idan Ta yi Watsi Da Yarjejeniyar Nukiliya.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Irak che ya ce: Yarjejeniyar Nukiliya an yi ta ne akan tubali mai karfi, ta yadda idan Amurka ta yi watsi da ita za ta cutu.

Sayyid Abbas Irak che wanda  shi ne mai kula da aiwatar da yarjejeniyar ta Nukiliya, ya fada a wani taro ta tattalin arziki anan Tehran a jiya litinin cewa: Shugaban Amurka Donald Trump ba zai iya ficewa daga cikin yarjejeniyar ta Nukiliya ba ta bangare daya, domin kuwa yarjejeniya ce ta kasa da kasa.

Iraki che ya ci gaba da cewa; Kasashen turai sun bayyana  ci gaba da bada goyon bayansu ga yarjejeniyar, kuma ga dukkanin alamu ita kanta Amurkan za ta ci gaba da aiki da ita, domin idan ba haka ba, kasashen turai din san sanar da cewa za su ci gaba da aiki tare da Iran.

Har ila yau, mataimakin ministan harkokin wajen na Iran, ya cel Karfin siyasar Iran da tsaro da jajurccewarta da ci gabanta na ilimi da fasahar Nukiliya, su ne su ka yammacin turai, musamman Amurka su ka kasa kawo wa Iran harin soja, ko kuma ci gaba da kakaba mata takunkumi.