Iran: Shugaban Kasa Rauhani Ya Dawo Gida Daga Ziyarar Kasar Rasha.
Shugaban Kasar Iran Hassan Rauhani ya dawo gida daga ziyarar da ya kai kasar Rasha.
Da safiyar yau laraba,shugaban Kasar Iran Hassan Rauhani ya dawo gida daga ziyarar da ya kai kasar Rasha.
Shugagan kasar ta Iran, ya gana da shugaba da kuma pira ministan kasar Rasha, inda su ka tattauna batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashe biyu.
Gabanin barowarsa kasar Rasha, Shugaba Hassan Rauhani ya fadawa manema labaru cewa: Da akwai dama mai yawa ta bunkasa alaka a tsakanin kasashen Iran da kuma Rasha, kuma gwamnatocin kasashen biyu suna azama mai karfi ta fadada alakar.
Har ila yau, shugaban na kasar Iran, ya kuma yi ishara da cewa a cikin shekaru biyu da suka wuce alakar Iran da kuma Rasha ta bunkasa a fagen yaki da ta'addanci domin tabbatar da sulhu da zaman lafiya a cikin wannan yankin da su ka hada a kasashen Syria da Iraki.
Hassan Rauhani ya tattauna da shugaban Velademir Putin akan halin da ake ciki a kasar syria da Iraki da Yemen da Afghanistan.