Shugaban Iran Yayi Kakkausar Suka Ga Harin St. Petersburg Na Kasar Rasha
(last modified Tue, 04 Apr 2017 16:49:43 GMT )
Apr 04, 2017 16:49 UTC
  • Shugaban Iran Yayi Kakkausar Suka Ga Harin St. Petersburg Na Kasar Rasha

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani yayi kakkausar suka ga harin ta'addancin da aka kai tashar jirgin karkashin kasa da ke Saint Petersburg na kasar Rasha da yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 14 da kuma raunana wasu sama da 50.

A cikin wani sakon ta'azziya da ya aike wa takwaransa na kasar Rashan, Vladimir Putin, shugaba Ruhani yayi Allah wadai da harin ta'addancin na Saint Petersburg yana mai isar da sakon ta'aziyyarsa ga shugaba Putin din da iyalan wadanda harin ya  ritsa da su.

Har ila yau shugaba Ruhanin ya sake jaddada aniyar gwamnatin Iran na hada kai da Rasha wajen  fada da duk wani nau'i na ayyukan ta'addanci kamar yadda ya zo cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaba Ruhani da shugaba Putin na Rasha a ziyarar baya-bayan nan da shugaban kasar Iran din ya kai kasar Rasha don kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shi dai wannan hari da aka kai shi a jiya yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 14 da kuma raunata wasu sama da 50, inda hukumomin tsaron kasar Kyrgyzstan suka bayyana cewar wani dan asalin kasar ne kai wannan harin.