Iran Da Pakistan Sun Tattauna Kan Matsalar Ta'addanci A Kan Iyakokin Kasashensu
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya zanta da fira ministan kasar Pakistan kan matsalolin tsaro musamman batun harin baya-bayan nan da 'yan ta'adda suka kai kan dakarun tsaron kan iyakar kasar Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif da tawagar da ke rufa masa baya da suka hada da manyan 'yan siyasa da na jami'an tsaro sun kai ziyarar aiki kasar Pakistan a yau Laraba, inda suka gudanar da zaman tattaunawa da mahukuntan kasar kan matsalolin tsaro musamman harin ta'addancin da wasu gungun 'yan ta'adda suka kai kan jami'an tsaron kan iyakar kasar Iran da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaron Iran masu yawa.
Har ila yau Muhammad Zarif Jawad ya kuma zanta da fira ministan Pakistan Chodari Nasr Ali Khan da ministan harkokin cikin gidan kasar ta Pakistan, inda dukkaninsu suka jaddada bukatar daukan matakan murkushe duk wasu ayyukan ta'addanci da suke addabar kasashen biyu.
A zaman tattaunawansa da mahukuntan kasar ta Pakistan: Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Zarif Jawad ya jaddada wajabcin warware matsalolin kan iyaka tsakanin kasashen biyu tare da daukan matakin gudanar da bincike da nufin zakulo 'yan ta'addan da suka kashe jami'an tsaron kan iyakar kasar Iran domin hukuntansu.