'Yan Majalisar Iran Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu Ga Kungiyar Hizbullah
(last modified Tue, 08 Mar 2016 05:44:55 GMT )
Mar 08, 2016 05:44 UTC
  • 'Yan Majalisar Iran Sun Sake Jaddada Goyon Bayansu Ga Kungiyar Hizbullah

Sama da 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran 200 ne suka nuna goyon bayansu ga kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da kuma yin Allah wadai da matsayar da kungiyar larabawan Tekun Fasha na sanya kungiyar cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.

A wata sanarwa da suka fitar a jiya Litinin, 'yan majalisar shawarar Musulunci ta Iran din su 222, cikin 'yan majalisar 290 sun yi Allah wadai da kuma kakkausar suka da wannan mataki da kungiyar Larabawan Tekun Fashan suka dauka a ci gaba da matsin lambar da suke yi wa kungiyar suna masu bayyana hakan a matsayin wani cin mutumci ga al'ummar kasar Labanon.

Sanarwar 'yan majalisar ta kara da cewa, a matsayinsu na wakilan al'ummar Iran, suna sake bayyana dukkanin goyon bayansu ga kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kasar Labanon da kuma jarumin shugabanta Sayyid Hasan Nasrallah, kamar yadda kuma suka bayyana kungiyar ta Hizbullah a matsayin wata alaka ta gwagwarmaya da jajircewa wajen fada da sahyoniyawa 'yan mamaya, wadanda suka ce idan da ba don kungiyar ba da har yanzu sahyoniyawan suna ci gaba da mamaye kudancin Labanon.

A ranar Larabar da ta gabata ce, kungiyar kasashen larabawan Tekun Fasha, da ta hada da kasashen Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, Bahrain da Kuwait, suka sanar da sanya kungiyar Hizbullah din cikin kungiyoyin 'yan ta'adda, lamarin da kungiyar ta yi watsi da shi sannan kuma al'ummomi da jami'an kasashe da yawa na larabawa da na musulmi suke ci gaba da Allah wadai da shi da kuma nuna goyon bayansu ga kungiyar ta Hizbullah.