António Guterres : Wajibi Ne A Kiyaye Yarjejeniyar Nukiliya
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ci gaba da cewa wajibi ne a kiyaye yarjejeniyar saboda kare zaman lafiya a duniya.
A baya mai dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya sha bayyana muhimmancin ci gaba da aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya.
Ita ma tarayyar turai ta bakin jami'ar kula da harkokin wajenta Federica Mogherini ta bayyana muhimmancin kare yarjejeniyar tare da jaddada cewa; Har yanzu hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa tana bayyana cewa Iran tana aiki da yarjejeniyar.
Bayan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi akan yarjejeniyar ta Nukiliya, majalisar kasar ta Congress tana da kwanaki 60 a gabanta domin daukar mataki akan ci gaba da kakabawa Iran takunkuman da aka dakatar da su saboda yarjejeniyar ta Nukiliya. Idan kuwar Majalisar ta Amurka ta kada kuri'ar amincewa da dawowar takunkumai akan Iran, to kasar za ta fice daga cikin yarjejeniyar.