Tafiye Tafiyen Jami'an Amurka A Saudiyya Hatsari Ne_ Zarif
(last modified Mon, 06 Nov 2017 18:56:11 GMT )
Nov 06, 2017 18:56 UTC
  • Tafiye Tafiyen Jami'an Amurka A Saudiyya Hatsari Ne_ Zarif

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Jawad Zarif , ya bayyana ziyarar aiki wanda shugawabannin gwamnatin Amurka suke yi zuwa Saudiyya duk masu hatsari ne ga yankin.

Zarif ya bayyana haka ne a shafinsa na tweeter a yau Litinin inda ya kara da cewa bayan ziyarar aikin da Trump ya kawo kasar saudia aka kara takurawa mutanen kasar Bahrai, sannan bayan da mai mai bashi shawara kan lamuran siyasa kuma surukinsa ya ziyarci kasar saudia, sai ga shi sa'ad alhariri na kasar Lebanon ya sauka daga kujerar Priministan kasar Lebanon a kasar ta Saudia, wanda ya nuna cewa suna kisa wata dasisa a yankin. 

Banda haka ministan ya kara da cewa gwamnatin kasar saudia tana ci gaba da yake yaken da taken wuce gona da iri ko kuma zalunci a kan mutanen kasar yemen da Bahrain.