Shugaba Rouhani Ya Taya Sabon Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa Murnar
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, saboda zabansa da aka yi.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar na Iran ta fitar ta ce a jiya Lahadi ne shugaba Rouhanin ya aike wa shugaban Cyril Ramaphosa wasikar taya shi murnar zabansa da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar Afirka ta Kudun inda yayi fatan alakar da ke tsakanin kasashen biyu zata ci gaba da karfafuwa a dukkanin fagage.
A ranar 15 ga watan Fabrairun nan ne dai 'yan majalisar kasar Afirka ta Kudun suka zabi Mr. Ramaphosa a matsayin sabon shugaban kasar don maye gurbin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma wanda ya sanar da yin murabus dinsa kwana guda kafin hakan.
Shugaba Zuma din dai yayi murabus din ne bayan matsin lambar da ya fuskanta daga wajen 'yan jam'iyyarsa mai mulki ta ANC wanda shugaba Ramaphosa din yake jagoranta bisa zargin rashawa da cin hanci da ake masa.