May 22, 2018 06:33 UTC
  • Sakataren Harkokin Wajen Britania Ya Sa Alamar Tambaya Kan Sharuddan Da Amurka Ta Shimfidawa Iran

Sakataren harkokin wajen kasar Britania Boris Johnson ya bayyana sharuddan da kasar Amurka ta shimfidawa Iran na ta cika su ko ta fuskanci fushinta a matsayin wadanda ba za su taba yiyuwa ba.

Tashar Talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Boris Johnson yana fadar haka ne a jiya litinin a taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G20 a birnin Buenos Aires na kasar Argentina. Ya kuma kara da cewa samun wani sabuwar tattaunawa dangane da matsalolin kasar Iran ba mai saki  bane. 

A jiya litinin din ne sabon sakataren harkokin wajen kasar Iran Mike Pompeo ya yi barazanar kakabawa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin da ba'a taba gani a tarihi ba idan bata cika sharudda guda 12 da ya shimfida mata ba. 

Johnson ya kara da cewa yerjejeniyar nukl;iya da aka cimma da kasar Iran , a nashi mahangar tana da kyau don ta amintar da duniya kan barazanar Iran ta mallaki makaman nukliya. Sannan yerjejeniyar ta budewa kasar Iran wasu hanyoyin kyautata tattalinn arzikin kasarta ba tare da wata matsala ba. Ficewa Amurka daga wannan yerjejeniyar wata babban kuskure ne inji shi.

 

Tags