Iran Ta Karyata Labarin Cewa Tana Tattaunawa Da H.K.Isra'ila
(last modified Tue, 29 May 2018 05:47:18 GMT )
May 29, 2018 05:47 UTC
  • Iran Ta Karyata Labarin Cewa Tana Tattaunawa Da H.K.Isra'ila

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya musanta labarin da wasu suke yadawa na cewa Iran tana tattaunawa ta bayan fage da haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar Jordan.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gida Radio da Talabijin na Iran ya bayyana cewar kakakin Ma'aiktatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne yayin da aka tambaye shi kan labarin da wasu kafafen watsa labaran "Isra'ila" da na Saudiyya suke yadawa kan cewa Iran tana tattaunawa ba ta kai tsaye ba da HKI, ya ce: Wannan wani labari ne maras tushe ballantana makama.

Mr. Qassemi ya ci gaba da cewa: Sakamakon irin cin amanar al'ummar Palastinu da wasu gwamnatocin larabawa suke yi, don haka kirkiro irin wadannan labaran wani kokari ne na wasa da hankula mutane.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: Iran dai ba ta yarda da haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin kasa ba, don haka manufar irin wadannan kararrakin a fili yake.