Rouhani Da Macron Sun Tattauna A Yau Ta Wayar Tarho
(last modified Mon, 27 Aug 2018 16:53:44 GMT )
Aug 27, 2018 16:53 UTC
  • Rouhani Da Macron Sun Tattauna A Yau Ta Wayar Tarho

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yau ya tuntubi shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ta wayar tarho, inda suka tattauna kan batutuwa daban-daban da suka shafi alaka tsakanin Faransa da Iran da kuma batun yarjejeniyar nukiliya.

kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yayin zantawar, Rouhani ya sheda wa Macron cewa, bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya, sauran banarorin da suka yi saura a cikinakwai babban nauyi a kansu, da hakan ya hada da kungiyar tarayyar turai.

Haka nan kuma ya ishara da cewa, kasashen da cikin yarjejeniyar a halin yanzu ya kamata su tabbatar wa duniya a aikace kan cewa suna nan daram wajen ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar ko babu Amurka.

A nasa bangaren shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sheda wa shugaba Rouhani cewa, kungiyar tarayyar turai tana nan daram a kan bakanta, kuma yanzu haka kungiyar tana yin nazari kan wasu lamurra da take shirin aiwatarwa, da suka shafi harkokin kasuwanci da kuma karfafa harkokin hada-hadar kudade tsakaninta da Iran, kamar yadda a nata bagaren kasar Faransa tana nan kan yarjejniyoyinta na kasuwanci da ta kulla da Iran.