Shugaba Hassan Rauhani Ya Dawo Gida Daga Taron Majalisar Dinkin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i33362-shugaba_hassan_rauhani_ya_dawo_gida_daga_taron_majalisar_dinkin_duniya
Shugaban na Jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi kwanaki biyar a birnin Newyork inda ya halarti taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma ganawa da shugabannin kasashe
(last modified 2018-09-27T12:52:50+00:00 )
Sep 27, 2018 12:52 UTC
  • Shugaba Hassan Rauhani Ya Dawo Gida Daga Taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban na Jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi kwanaki biyar a birnin Newyork inda ya halarti taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma ganawa da shugabannin kasashe

Bugu da kari shugaba Rauhani ya kuma yi hira da kafafen watsa labaru na Amurka da suka hada da tsahar talabijin din CNN. Shugaba Hassan Rauhani ya bijiro da matsayar jamhuriyar musulunci ta Iran akan batutuwa daban-daban.

A yayin da yake jawabi a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, shugaban na Iran ya yi magana akan cewa Iran ba ta bukatuwa da shimfida ikonta akan wasu kasashe, abin da yake gabanta shi ne kulla kawance mai kyau.