Oct 03, 2018 11:51 UTC
  • Hukumar OFCOM Ta Fara Bincike Wata Tashar Talabijin Mai Goyon Bayan Yan Ta'adda A London

Hukuma mai kula da kafafen yada labarai Ofcom a takaice a kasar Britania ta fara bincike don gano gaskiyan zargin da JMI ta yi na cewa tashar Talabijin ta "Iran International" ta sabawa dokokin watsa labarai a kasar ta Britania.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani jami'an hukumar Ofcon yana fadawa jaridar Guardina ta kasar Britania a ranar litinin da ta gabata. Jami'an ya bayyana cewa binciken yana da matukar muhimmanci a wajensu. 

Kimanin makonni biyu da suka gabta ne Yaakub Hor Al-Tustari kakakin kungiyar yan ta'adda ta Al-ahwaziyyah ya yi hira ta tashar talabijin ta "Iran International" mai watsa shirye-shiryenta da harshen farisanci kuma wacce kasar Saudia ta kafa a birnin London na kasar Britani inya ya nuna goyon bayansa ga kisan gillan da wasu yan ta'adda guda hudu suka yi wa mutane a birnin Ahwaz wadanda suke kallon faretin da sojojin JMI suke yi a cikin garin, an kashe mata da yara da sojoji 24 a wannan harin. Jim kadan bayan hirar ne jakadan kasar Iran a London ya shigar da korafi a gaban hukumar ta Ofcom.

 

Tags