Dec 25, 2018 07:44 UTC
  • Shugaban Kasar Iran Ya Aike Da Ta'aziyya Ga Iyalan Aya. Sayyid Hashimi Sharudi

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhuni ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan Aya. Hashimi Shahrudiya shugaban majalisar maslahar tsarin mulkinn JMI kum tsohon alkalin alkalan kasar wanda Allah yayiwa rasuwa a jiya da yamma.

Shugaban kasar ya kara da cewa rasuwar Aya. Hashimi Shahrudi wani babban rashi ne ga al-ummar Iran da kuma iyalansa, har'ila da kuma makarantun addinin a nan JMI.

Ruhani ya ce Aya. ya bar ayyukan na alkhairi da dama wa al-ummar iran, bayaga daliba da ya karantar shi ne ya kafa Jami'ar Adali da kuma tsarin nan da kyautata dangantaka tsakanin jami'o'i da kuma makarantun ilmin addinin a kasar Iran. 

Banda haka Aya Hashimi Shahrudi ya rike mukamin alkalin alkalai na JMI na tsawon shekaru goma, kafin a bashi shugaban majalisar masalar tsarin mulki a nan Iran, mukamin da yake rike da shi har zuwa rasuwarsa a jiya Litinin yana dan shekara 70 a duniya.

Tags