Iran:An Fara Atsayin Soja A Jihar Isfahan
Sojojin kasa na jamhoriyar musulinci ta Iran sun fara gudanar da wani gagarimin atisayin soja na shekarar 1397 yau juma'a a jihar Isfahan dake tsakiyar kasar
Hukumar gidan radio da talabijin din kasar Iran ta habarta cewa manufar wannan atisayin sojojin kasar shine gabatar da sabin sauye-sauyen da aka gudanar a jerin dakarun tsaron kasa, kuma kimanin sojoji dubu 12 ne suka halarci wannan atisayi.
A yayin atisayin an gabatar da sabin kayan yaki na zamani kama daga manyan motoci masu silke, sabin motocin yaki da kuma na'urori aikin soja da sauransu.
A matakin farko na Atisayin mai taken Iktidar 97, sojoji sun samu nasarar gano wani jirgin sama maras matuki tare kuma da kakkabo shi daga sararin samaniya.
Sojojin sun fara gudanar da Atisayin ne cikin jarimta da gwada kwarewa, ta yadda suka kai farmaki cikin sauri tare kuma kare kai daga harin abokanin gaba.