An Gudanar Da Taro Kan Rasuwar Imam Khumaini A Hubbaren Sayyida Zainab
An gudanar da taron tunawa da cika shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khomenei a hubbaren Sayyida Zainab da ke birnin Damascus an kasar syria
Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, Ibrahim Amin Sayyid shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hizbullah ta Lebanon tare da wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin palastinawa yan gwagwarmaya mazauna birnin duk sun halarci zaman taron.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin, Ibrahim Amin sayyid ya bayyana cewa, gwagwarmayar da al'ummar kasar Lebanon suke da kuma irin nasarorin da suka samu kan makiya musamman ma yahudawan sahyuniya, sakamako ne na abin da Imam khomenei ya gina, kamar yadda suma palastinawa irin nasarorin da suke samu a kan yahudawa sakamakon darussan da suka dauka daga gare shi ne.
Sheikh Muhammad Nasiri shugaban ofishin jagoran juyin juya halin muslunci na Iran a kasar Syria ya gabatar da nasa jawabin, inda ya bayyana Imam Khomenei da cewa shi mutum da ya kasance na dukaknin al'ummomi, kuma kalamai da rubuce-rubucen da masana suka yi a kansa a dukkanin sassa na duniya ya isa zama bababn dalili kan hakan.
Daga karshe ya ce bababn abin da Imam ya koyar da al'umma shi ne dogaro da Allah da himma da kuma rashin mika kai ga azzalumai yan mulkin mallaka, da kuma dagewa kan hakan, ya ce idan har mutane suka yi aiki da wannna kouatrawa to za su rayu a cikin yanci.