Ganawar Ministan Harkokin Wajen Iran Da Sabon Shugaban Lebanon
(last modified Tue, 08 Nov 2016 08:03:35 GMT )
Nov 08, 2016 08:03 UTC
  • Ganawar Ministan Harkokin Wajen Iran Da Sabon Shugaban Lebanon

A daren jiya ne ministan harkokin wajen kasar Iran Muhamamd jawad Zarif ya gana da sabon shugaban kasar Lebanon Michel Aun a fadarsa da ke birin Beirut.

A yayin ganawar, shugaban kasar ta Lebanon ya bukaci a kara fadada alaka tsakanin Iran da Lebanon a dukkanin bangarori na siyasa, tattalin arziki har ma da na tsaro, da kuma bangaren ilimin kimiyya da fasa.

Haka nan kuma shugaban na Lebanon ya bukaci da a hada karfi da karfe wajen yaki da babbar barazanar ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya, tare da fatan ganin an warware rikicin kasar Syria ta hanyoyi na lumana.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya yi wa shugaba Aun tare da al'ummar kasar Lebaon baki daya fatan alkhairi da nasara, tare da bayyana shirin kasarsa na yin aiki kafada da kafada tare da kasar Lebanon a dukkanin bangarori.

A yau ne Zarif zai gana da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon Nabih Birri, da kuma Firayi minista Sa'ad Hariri.