Yarjejjeniyar Tsagaita wuta a Yemen
(last modified Thu, 17 Nov 2016 18:14:05 GMT )
Nov 17, 2016 18:14 UTC
  • Yarjejjeniyar Tsagaita wuta a Yemen

An fara gudanar da yarjejjeniyar tsagaita wuta a kasar Yemen

Duk da irin adawar da Gwamnatin Abdu Rabahu Mansur Hadi shugaban kasar da ya yi murabus ta yi, a yau 17 ga watan Nuwamba, an fara zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta tsakanin Kungiyar Ansarul... ta kasar Yemen da masarautar Ali sa'oud, da farko dai an bayyana cewa Gwamnatin Mansur Hadi ta bayyana adawarta da yarjejjeniyar tsagaita wutan, to saidai bayan matsin lamba daga masarautar Ali sa'oud ta amince da ita.

Wasu rahotanni sun ce Jiragen yakin kawancen Saudiyan sun kai farmaki kan sansanin Dakarun Ansarul... a birnin Sana'a fadar milkin kasar.

A bangare guda Ma'aikatar harakokin wajen Iraki ta yi marhabin da wannan yarjejjeniya tare da ta bayyana ta a matsayin wata nasara na warware rikicin kasar yemen din ta hanyar Siyasa. Bangarorin biyu dai sun amince su zauna kan tebirin shawara domin kokarin kafa Gwamnati hadin kan 'yan kasa.

Sama da shekara guda kenan da kawancen Saudiya bisa goyon bayan kasar Amurka da wasu kasashen Laraba ke kai hare-haren wuce gona da iri kan Al'ummar kasar Yemen, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar Mutane sama da dubu goma aksarinsu Mata, kananen yara gami da tsofofi.