Shirin Gwamnatin H.K.Isra'ila Na Ci Gaba Da Gine-Ginen Matsugunan Yahudawa
Duk da matakin da kungiyoyin kasa da kasa suka dauka na yin Allah wadai da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da gine-ginen da ta yi a yankunan Palasdinawa da ta mamaye, a halin yanzu haka ma tana shirin ci gaba da gudanar da wasu gine-ginen a yankunan na Palasdinawa.
Cibiyar watsa labaran Palasdinawa ta nakalto daga tashar talabijin ta haramtacciyar kasar Isra'ila a jiya Asabar cewa: Majalisar ministocin gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra'ila zata kada muri'ar amincewa da gina wasu sabbin gidaje 770 a matsugunin yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida da ke garin Jilo a gabar yammacin kogin Jordan.
Rahotonni sun bayyana cewa tun a shekara ta 2013 gwamnatin ta haramtacciyar kasar Isra'ila take da shirin gudanar da gine-ginen amma ta fuskanci turjuya daga kungiyoyin kasa da kasa lamarin da ya sanya alatilas ta dakatar da shirin, amma a halin yanzu ta sanar da aniyarta ta aiwatar da kudurin bayan sake samun amincewar majalisar ministocin kasar.